Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.
January 10, 2022An bude gasar cin kofin Afrika karo na 33 a KamaruShirin Duniyar Wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali kan gasar cin kofin Afrika da aka fara gudanarwa jiya lahadi a Kamaru, gasar a wannan karon na matsayin karo na 33 tun bayan farowa zuwa yanzu....more11minPlay
January 03, 2022An kammala gasar kwallon dawaki ta bana a JosShirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yada zango ne a garin Jos da ke jihar Filato ta Najeriya, inda aka kammala wasannin gasar kwallon dawaki da aka fi sani da Polo a Turance, gasar da ta samu halartar baki daga ciki da wajen Najeriya. Bashir Ibrahim Idris ya halarci gasar ta tsawon mako guda. Ku latsa alamar sautin domin sauraren cikakken shirin da ya hada....more10minPlay
December 27, 2021Kalubalen da ke tunkaro gasar cin kofin Afrika na 2022 a KamaruShirin Duniyar wasanni na wannan mako tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali kan shirin tunkarar gasar cin kofin Afrika da za ta gudana a Kamaru da kuma jita-jitar da ke nuna cewa da yiwuwar kungiyoyi su hana 'yan wasan nahiyar halartar gasar....more11minPlay
December 20, 2021Hukumar kwallon kafar Najeriya ta sauya mai horar da kungiyar Super EaglesHulumar kwallon kafar Najeriya NFF ta sallami Gernot Rhor mai horar da kungiyar kwallon kafar Super Eagles.Sallamar dake zuwa a wani lokaci da ya kasa kawo sauyi a tafiyar kungiyar ga baki daya.a cikin shirin Abdurahaman Gambo Ahmad ya ji ta bakin ma'abuta kwallon kafa da kuma irin fatan su bayan nadin sabon mai horar da Super Eagles a cikin shirin Duniyar wasanni....more10minPlay
December 13, 2021Yadda wasu kasashe ke shirin kauracewa gasar Olympics ta Beijing 2022Shirin Duniyar wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali kan yadda wasu kasashe ke kokarin kauracewa gasar Olympics ta hunturu da za ta gudana a birnin Beijing na China cikin shekarar 2022....more11minPlay
December 06, 2021Wasu na ganin kyautar Balon d'Or ta rasa tagomashi a yanzuA cikin shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako, Adurrahman Gambo Ahmad ya duba batun kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa ta duniya ta Balon d'Or da dan wasan PSG Lionel Messi ya lashe kwanan nan, inda wasu masu sharhi ke ganin ta rasa tagomashinta....more10minPlay
November 29, 2021Matsayar masana kan shirin fara amfani da fasahar VAR a kwallon kafar AfirkaShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan rana tare da AbduRahman Gambo Ahmed ya tattauna da masana harkar wasanni akan shirin hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka CAF, kan shirin fara amfani da fasahar taimkawa alkalin wasa ta VAR yayin wasanni a nahiyar....more11minPlay
November 22, 2021Kokarin kasashe na neman tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya a QatarShirin Duniyar Wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali kan yadda kasashen Duniya ke ci gaba da kokarin samun tikitin zuwa Qatar ciki har da Najeriya da ke dakon wasan cike gurbi don samun nata tikitin. Ayi saurare Lafiya....more11minPlay
November 15, 2021Yadda kungiyoyin kwallon kafar Turai ke raba gari da koca kocai a kakar banaShirin 'Duniyar Wasanni na wannan mako tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazara dangane da yadda kungiyoyin kwallon kafar Turai ke raba gari da masu horas da tawagoginsu, inda kawo yanzu sama da koca-kocai 10 suka rabu da aikinsu a kakar bana, yayin da wasu ke cikin tsaka mai wuya....more11minPlay
November 09, 2021Ganduje ya ware kusan Naira miliyan 100 don farfado da kwallon kafaShirin Duniyar Wasanni tare da Abubakar Isa Dandago ya tattauna ne game da bunkasa kananan kungiyoyin kwallon kafa a jihar Kano ta Najeriya, inda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ware kusan Naira miliyan 100 domin tallafa musu....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.