Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
October 03, 2016Nazari kan gasar cin kofin Duniya ajin mata a kasar JordanShirin ya maida hankali kan gasar cin Kofin Duniya da ke gudana a kasar Jordan, ajin mata 'yan kasa da shekaru 17....more11minPlay
September 26, 2016Manyan wasannin Premier a karshen makoShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan manyan wasannin da aka yi tsakanin Manchester United da Leceister City daa kuma Arsenal da Chelsea a gasar Premier ta Ingila, in da muka zanta da magoya bayan kungiyoyin jim kadan da kammala fafatawar ta ranar Asabar....more11minPlay
September 19, 2016Najeriya ta taka rawa a gasar nakasassu a RioShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan nasarar da Najeriya ta samu a gasar nakasassu da aka gudanar a birnion Rio na Brazil, in da ta lashe lambobin yabo 12 da suka hada da zinari 8 da azurfa 2 da kuma tagulla 2....more10minPlay
September 16, 2016Tasiri ko akasin kafa dokar ta baci a harkar wasannin NajeriyaIdan za’a iya tunawa dai a ranar daya ga watan Satumba Ministan harkokin wasanni na Najeriya Barrister Solomon Dalung ya bayyana kafa dokar ta baci a harkar wasannin kasar lokacin da ya karbi rahoton kwamitin da aka kafa kan samar da gyara a harkar wasannin Najeriya. A cewar Ministan wasannin babban dalilin da yasa shi kafa dokar ta bacin shi ne yadda Najeriya ta gaza tabuka komai in banda kwallon kafa a gasar Olympics da aka kammala Brazil.Shirin ya duba tasirin kafa dokar ta bacin da kuma sauran batutuwan wasanni musamman wasannin Paralympics wato na nakasassu da ke gudana a birnin Rio na Brazil....more10minPlay
August 29, 2016Rawar da 'yan wasan Najeriya suka taka a wasannin OlympicsMinistan wasannin a Najeriya Solomon Dalung ya yi bayyanin kalubalen da 'yan wasan Najeriya suka fuskanta a shirye shiryen zuwa gasar Olympics da aka kammala kwanan nan a birnin Rio na kasar Brazil....more10minPlay
August 22, 2016An kammala gasar wasannin Olympics na Rio 2016Bayan kwashe kwanaki 16 da soma wasannin gasar Olympics, a jiya an kammala gasar da kasaitaccen biki a filin wasa na Maracana dake birnin Rio, Abdoulaye Isa ya tattaro mahinman batutuwan da suka gudana a gasar a cikin shirin duniyar wasanni....more11minPlay
August 19, 2016Amurka ce da yawan lambobin yabo a Rio OlympicsShirin Duniyar Wasanni ya tattauna ne kan wasannin Olympics da ake gudanarwa a Rio na Brazil. Shirin ya tattauna da masana kan wainar da ake toyawa a Rio....more10minPlay
August 12, 2016Tattauna batun tsaro da yadda gasar Olympics ke gudanaShirin ya maida hankali kan yadda ake cigaba da fuskantar matsalar tsaro a gasar Olympics, da kuma yadda hakan ka iya shafar makamnciyar gasar mai zuwa....more10minPlay
August 08, 2016Nazari kan wasannin Olympics dake gudana a birnin RioWasannin Olympics dake hada kawunan kasashen duniya sama da 200 ya soma ne a ranar Juma'ar da ta gabata, Abdulrahman Gambo Ahmad ya bi diddingin gasar acikin shirin Duniyar Wasannin na wannan makon....more10minPlay
August 05, 2016Tattaunawa bisa matsalolin da Olympics ke fuskantaYayin da aka shiga cikin gasar Olympics ta 2016 gadan gadan a birnin Rio na Kasar Brazil, shirin ya tattauna da Masana da kuma masu ruwa da tsaki kan harkar wasanni game da tasirin kalubalen da kasar Brazil ke fuskanta zai yi wajen rage armashin gasar.Filin na Duniyar wasanni ya tattauna da Tsohon dan wasan Super Eagles Garba Lawal, da kuma Aminu Sani Sado mai sharhi kan al'amuran wasanni....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.