Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
June 17, 2016Tsoffin 'yan wasan Najeriya sun yi wasa a BauchiShirin duniyar wasanni tare da Ramatu Garba Baba na wannan makon ya tattauna ne kan tsoffin 'yan wasan Najeriya na Super Eagles da suka yi wasan kwallon kafa a jihar Bauchi a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa domin neman kudin da za a tallafa wa 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya. Daga cikin wadanda suka buga wasan akwai Kanu Nwanko da Tijjani Babangida da Victor Ikpeba da dai sauransu....more11minPlay
June 10, 2016Faransa za ta bude gasar cin kofin Turai 2016Shirin Duniyar Wasanni ya tattauna ne game da gasar cin Kofin Turai da za a fara a ranar Juma'a 10 ga watan Yuni cikin tsauraran matakan tsaro. Sannan shirin ya tabo batun jana'izar tsohon zakaran Damben Boxing Muhammad Ali da kuma mutuwat tsohon kocin Najeriya Stephen Keshi da ya rasu a ranar Laraba....more11minPlay
June 06, 2016Mutuwar gwarzon dambe Mohammed AliDubban mutane daga sassan duniya ne za su halarci jana’izar tsohon zakarar damben duniya Muhammad Ali bayan rasuwarsa a ranar juma’ar da ta gabata a wani asibiti dake Arizona...more11minPlay
May 30, 2016Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai karo na 11Shirin Duniyar Wasanni ya tattauna ne kan nasarar da Real Madrid ta samu na lashe kofin gasar Zakarun Turai karo na 11 bayan ta doke Atletico Madrid a bugun fanariti a wasan karshe da suka fafata a Milan....more11minPlay
May 20, 2016Kalubalin dake gaban Fatma Samoura sabuwar sakatariyar hukumar FIFAShirin duniyar wasanni a wannan lokaci ya mayar da hankali kan kalubalin dake gaban sabuwar sakatariyar hukumar kwallon kafa ta duniya Fatma Samoura 'yar asalin Senegal, kana a cikin shirin an duba gasar wasanni tsakanin matasa 'yan gudun hijiran Boko Haram a arewacin Najeriya. A yi sauraro lafiya tare da Ramatu Garba Baba....more11minPlay
May 16, 2016Sharhi kan yadda aka kammala Lig Lig a TuraiShirin Duniyar Wasanni ya yi nazari ne kan yadda aka kammala wasannin Lig lig na Turai....more11minPlay
May 09, 2016Wasan karshe tsakanin Real Madrid ta AtleticoShirin duniyar wasanni tare Umaimah Sani Abdul'mumin ya tattauna ne akan wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai, inda Real Madrid za ta kara da makociyarta Atletico Madrid a ranar 28 ga wannan wata na Mayu a Milan na Italiya....more11minPlay
May 06, 2016Fifa ta tuna da marigayi Yekini na NajeriyaA cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Intanet, hukumar FIFA ta tuna da kwallon da Yekini ya jefa a ragar kasar Bulgaria a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Amurka a shekara ta 1994.Wannan kwallon dai, ita ce ta farko da Najeriya ta ci a gasar cin kofin duniya, yayin da Yekini ya shiga cikin ragar yana girgizata, yana kuka domin nuna farin cikinsa na zura wannan kwallo mai cike da tarihi.Ya dai rasu a ranar 4 ga watan mayun shekarar 2012 bayan ya yi fama da rashin lafiya. Sannan ya bar duniya yana da shekaru 48 da haihuwa.Ramatu Garba Baba ta yo mana dubi a kai tareda kawo wasu labaren wasanni a cikin shirin Duniyar Wasanni....more10minPlay
May 02, 2016Barazanar ficewar Birtaniya ga Kwallon kafa a TuraiShirin Duniyar Wasanni ya yi nazari ne game da barazanar ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai ga harakar kwallon kafa a Nahirar....more11minPlay
April 29, 2016wasanni a rayyuwar matasa a NajeriyaA cikin shirin duniyar wasanni ,Ramatu Garba ta maida hankali kan sakamakon bicinke da aka gudanar a Najeriya tareda baiwa yan kasuwa dama kamfanoni damar zuba makuden kudade a duniyar wasanni....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.